Sep 18, 2018 18:57 UTC
  • Najeriya: An Kashe Wata Ma'aikaciyar Agaji Na Kungiyar Red Cross

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato kungiyar agajin ta Red Cross tana cewa; Ma'aikaciyar Agajin an sace ta ne tun a farkon shekarar nan nan ta 2018 a garin Kala Balge da ke jahar Borno

Kungiyar ta Red Cross ta yi tir da kisan da aka yi wa ma'aikaciyar tasu, tare da yin kira da a saki wasu ma'aikatan biyu da ake ci gaba da garkuwa da su.

Kungiyar Boko haram ce dai ake zargi da sacen ma'aikatan agajin da kuma yi wa daya daga cikinsu kisan gilla.

Wannan kungiyar ta fara kai hare-haren ta'addanci ne a yankin arewa maso gabacin Najeriya tun a cikin shekarar 2009 wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 20,000, sannan kuma da tilastawa wasu mutane miliyan biyu da 600,000 yin hijira.

Tags