Sep 19, 2018 12:33 UTC
  • An Sace Wani Dan Kasar Italiya A Nijer

Hukumomin birnin Yamai sun tabbatar da sace wani Limamin coci dan kasar Italya a kan iyakar kasar da Burkina Faso

Cikin sanarwar da hukumomin kasar Nijer din suka fitar sun  ce a tsakiyar daren ranar Talata ce wasu mutane akan babura suka kai farmaki gidan Limamin cocin mai suna Pier Luigi Maccalli da ya shafe tsawon lokaci yana aikin addini a yankin Makolandi da ke da tazarar kilo mita 130 a yamma maso kudancin kasar 

Kakakin gwamnatin Nijer Malam Zakariya Abdourahamane ya ce jami’an tsaron Nijar sun bazama neman ceto malamin kiristan.

Yankin Tillabery da aka sace dan Italyan yankin ne da ke Makwabtaka da Mali da Burkina Faso kuma yanki ne da ke fuskantar hare haren yan ta’adda da ke gwagarmaya da makamai daga kasar Mali.

A 'yan watannin da suka gabata ma wasu mahara sun sace wani dan kasar Jamus da ke aikin Jinkai a yanki Ayerou  na kasar da ke makwabtaka da kasar Mali.

Tags