Sep 27, 2018 19:26 UTC
  • Cutar Kwalara Ta Salwanta Rayukan Mutum 67 A Nijer

Ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar Nijer ta sanar da mutuwar mutum 67 sanadiyar cutar kwalara a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar nijer a wannan alhamis na cewa duban mutane ne a kasar suka kamu da cutar kwalara a kasar musaman ma a  jahar maradi, kuma ya zuwa mutum 67 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wannan cuta.

Ministan ya ce cutar ta fara billa ne a jahar Maradi dake iyaka da Najeriya daga kudancin kasar, inda aka tabbatar da kamuwar mutum dubu uku da 232 a jahar kafin daga bisani ta billa zuwa wasu yankunan kasar.

Kafin billar cutar a jahar maradi, rahotani sun ce cutar ta fara billa a yankin Jibiya na jahar Katsina bayan ambaliyar ruwa da yankin ya fuskanta, lamarin da ya hallaka mutane da dama da kuma raba wasu rasu dariruwa da mahalinsu.

Bisa Rahoton MDD, a ko wata shekara,kimanin mutum miliyan biyu da dubu 900 ne  ke kamuwa da cutar kwalara a Duniya kuma daga cikinsu kimanin mutum dubu 95 ne ke rasa rayukansu.

Tags