Oct 01, 2018 05:42 UTC
  • Nijar Ta Maido Da Harajin Kiran Waya Na Kasa Da Kasa

Gwamnatin Jamhuriya Nijar, ta ce zata dawo da haraji kan kira waya na kasa kasa, a shekara ta 2019 mai zuwa, bayan soke hakan a shekarar nan ta 2018.

Gwamnatin dai na zargin kamfanonin sadarwa na wayar salula da kin mutunta alkawarin da suka dauka na inganta aikin nasu da hanyoyin sadarwarsu, saidai basu yi hakan ba a cewar ministran kudi na kasar Hasumi Masaudu'

Harajin dai na kunshe ne a cikin kasafin kudin kasar na shekara ta 2019, da ministan kudi na kasar ya gabatarwa majalisar dokoki.

Za'a dai fidda haraji na CFA 50 zuwa 88, a ko wanne minti guda ga duk wani kira mai shigowa na kasa da kasa, kamar yadda kudirin kasafin kudin gwamnatin kasar ya tanada, wanda kuma aka mikawa majalisar dokokin kasar domin neman amincewa.

Harajin dai na kawo wa ma'aikatar harajin kasar kudade da yawansu ya kai kimanin Biliyan ashirin na kudin CFA, kwatancin Yuro Miliyan talatin. 

Tags