Oct 01, 2018 19:03 UTC
  • Malaman Jami'a A jumhuriyar Niger Sun Kawo Karshen Yajin Aiki

Malaman jami'a a jumhuriyar Niger sun kawo karshen yajin aikin da suka shiga kimain wata guda da ya gabata don neman albashinsu da kuma wasu bukatu da suka shafi harkar gudanarwa na jami'o'in kasar.

Jaridar Punch ta Najeriya ta bayyana cewa an bude karatu a jami'oin kasar Niger a yau Litinin bayan da kungiyoyin malaman jami'o'i a kasar suka bada sanarwan dage yajin aikin da suka soma tun kimanbi wata guda da ya gabata.

Nabala Adare babban sakataren kungiyar shugaban kungiyar "National Union of Teacher-Researchers in Higher Education" ko SNECS ya bayyana kamfanin dillancin labaran AFP kan cewa yayan kungiyarsa masu biyayya ne don haka sun koma bakin aiki a yau litinin.

Sai kuma Idder Algabid shugaban kungiyar daliban Jami'a na kasar ya ce an bude karatu a dukkan sassa na jami'o'i a kasar, sai dai har yanzun wasu daliban basu sami tsarin karatun da zasu yi na wannan sabuwar shekarra karatu ba. 

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta janye batun nada shuwagabannin jami'o'in kasar kamar yadda ta so, bayan da suka amincewa juna tare da malaman jami'o'in kasar.

 

Tags