Oct 01, 2018 19:04 UTC
  • An Kashe Mutane Akalla 20 A Kan Iyakokin Niger Da Mali

Mutane akalla 20 ne aka tabbatar da mutuwar a kan iyakokin kasashen Niger da Mali

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar jami'an tsaron kasar Mali tana cewa wasu yan bindiga wadanda ba'a tantancesu har yanzun ba sun kashe mutane 20 daga kabilar buzaye a kusa da kan iyakar kasar da kasar Niger.

Har yanzun cikekken labari dangane da harin baia bayyana ba, amma fadan da aka yi a ranar asabar a wannan yankin mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu. 

Yan kabilar buzaye dai mutane ne masu yawo zuwa wurare daban daban, a yankin yammacin Afrika amma a kasar Mali sune suka yi yawa a arewacin kasar har ma suna son kafa kasa mai suna Azawad. Bayan juyin mulki na shekara ta 2012 a kasar Mali buzayen arewacin kasar sun so shelanta kafa kasar Azawad amma shigowar yan ta'adda masu kishin addini a cikin lamarin ya bata masu wannan shirin.

 

Tags