Oct 03, 2018 17:55 UTC
  • Nijar Ta Kori Likitar (Doctors Without Borders), Saboda Zuzuta Alkalumman Mace Macen Yara

Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun sanar da korar wata likitar yara ta kungiyar likitoci marar iyaka wato (Doctors Without Borders) ta Switzerland, saboda zarginta da azuzuta alkalumman mace-macen yara kanana a garin Magaria dake jihar Zinder.

An baiwa ma'aikaciyar mai suna Dakta Anne Pitter wa'adin sa'o'i 24 ta kwashe nata ye nata ta bar kasar.

Hukumomin kiwon lafiya na kasar sun ce likitar ta yi karya ne a game da hoton bidiyon da kungiyar ta (Doctors Without Borders) ta wallafa a shafukan sada zumunta, inda likitar ta bayyana cewa yara goma ne ke mutuwa ko wacce rana, kimanin  298 zuwa 300 a cikin wata guda, a asibitin na Magaria, sakamakon kamuwa da cutar Malaria da rashin abinci mai gina jiki.

Ministan kiwon lafiya na kasar, Dakta Illiasu Idi Mai Nasara, wanda ya ziyarci asibitin ya ce babu wata shaida data nuna alkalumman mace macen yaran kamar yadda ma'aikaciyar ta bayyana.

Ministan ya kara da cewa matakin bai shafi kungiyar ta (Doctors Without Borders) ba, saboda shugabannin kungiyar sun ce ba da sunansu ma'aikaciyar ta yi magana ba.

Tags