Oct 06, 2018 12:58 UTC
  • Kungiyar Boko Haram Ta Kaddamar Da Hari Kan Sansanin Sojin Kasar Chadi

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan sansanin sojin kasar Chadi da ke kusa da kan iyaka da Nigeriya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto daga majiyar rundunar sojin kasar Chadi a jiya Juma'a cewa: Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun harba makamai masu linzami kan sansanin sojin Chadi da ke kudancin garin Kaiga-Ngouboua kusa da kan iyaka da kasar Nigeriya, inda suka jikkata soja guda tare da jikkata wani na daban.

A watan Satumban da ya gabata ma 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin wuce gona da iri kan sojojin na Chadi a kusa da tafkin Chadi, inda suka kashe sojojin Chadi biyu, sannan a martanin da sojojin suka mayar kan maharan sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda goma sha bakwai.

Tags