Oct 16, 2018 06:31 UTC
  • An Kara Karfafa Tsaro A Kan Iyakokin Najeriya Da Nijer

Gwamnatin jumhuriyar Nijer ta kara karkafa harkokin tsaro a kan iyakarta fa tarayyar Najeriya

Kamfanin dillincin labaran Xinhua na kasar China ya nakalto labari daga ma'aikatar cikin gida na Jumhuriyar Nijer tana fadara haka a jiya Litinin ta kuma kara da cewa saboda karuwar tabarbarewa harkokin tsaro a kan iyakokin Najeriya da Nijer a cikin yan watannin da suka gabata ma'aikatar ta ga yakamata ta dauki matakin. 

Ma'aikatar cikin gida ta Jumhuriyar Nijer ta kara da cewa matsalolin dai sun hada da fashi da makami da garkuwa da mutane don karban kudaden fansa wadanda suka kara yawa a cikin yan watannin da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa a cikin yan makonnin da suka gabata jami'an tsaro na ksashen biyu a wani aikin hadin guiwa sun wargaza kungiyoyi masu aikata laifi har 12 a yankin. 

Tarayyar Najeriya da Nijer dai suna hada kan iyaka mai tsawon kilomita 1500. Tun kafin haka dai kasashen Nijeriya, Nijer, Chadi da kuma Kamaru sun kafa rundunar hadin guiwa don yaki da ayyukan yan ta'adda ta kungiyar Boko Haram.

Tags