Oct 17, 2018 18:55 UTC
  • Jami'an Tsaron Libiya Sun Kame Wasu Gungun 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish A Kasar

Jami'an tsaron gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun kame gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin kudancin garin Sirt na kasar.

Majiyar tsaron gwamnatin hadin kan kasar Libiya a yau Laraba ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a samamen da suka gudanar a yankin kudancin garin Sirt.

Mahukuntan Libiya sun sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun fara gudanar da wani samame ne a yankunan garin na Sirt da nufin tsarkake su daga samuwar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish.

Tun bayan da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta fara shan kashi a kasashen Siriya da Iraki ta dauki matakin fara kafa babban sansaninta a garin Sirt na kasar Libiya amma rundunar tsaron Libiya ta daura damarar yaki kan kungiyar tare da samun nasarar rusa karshen tungarta a karshen shekara ta 2016.

Tags