Oct 20, 2018 11:08 UTC
  • Nijar : Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Sha'anin Noma

Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda ke cewa mastalar da ake fama da ita a wasu yankunan dake karkashin dokar ta baci a Nijar, na iya hadassa koma baya wajen samun albarkacin gona.

Yankunan sun hada da arewacin jihohin Tillaberi, Tahoua da kuma Diffa), wandanda suka jima karkashin dokar ta baci saboda matsalolin tsaro da suka hada dana mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kuma Boko Haram a jihar Diffa inji rahoton na PAM.

rahoton ya kara da cewa an samu sabkar ruwa sosai a damanar da ake shirin ban kwana da ita, saidai matsalar tsaro ta kasance babban kalubale wajen yin shuka.

Tags