Oct 21, 2018 19:01 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Manoma 12 A Jahar Borno

Kungiyar ta'addancin nan ta Boko haram ta kashe manoma 12 a jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Mayakan kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun kashe manoma 12 a kauyen Kalle da ke wajen birnin Maiduguri na jihar Borno ta hanyar yi musu yankan rago da wuka.

Rahotanni sun ce mayakan sun isa kauyen na Kalle ne mai nisan kilomita 17 da birnin Maiduguri jiya Asabar lokacin da manoman ke aikinsu na gona.

Wani manomi cikin mutane 3 da suka tsira da rayukansu a harin, ya bayyana cewa  lokacin da suka ji tsayawar motocin mayakan ne kowannensu ya ranta ana kare amma suka bisu suka kamo su.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar Boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, sannan a shekarar 2015, kungiyar ta fadada hare0harenta zuwa kasashen Kamaru da Tchadi da Nijeri, kuma kawo ya zuwa yanzu yayi  sanadiyar salwantar rayukan mutum sama da dubu 20 sannan ya raba wasu sama da milyan daya da dubu 600 da mahalinsu.

Tags