Antonio Gutrres Ya Jaddada Wajabcin Karfafa Ayyukan MDD A Kasar Afirka Ta Tsakiya
Oct 23, 2018 18:59 UTC
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya gabatarwa da Majalsar
Kamfanin dillancin labarun Faransa wanda ya ambato rahoton Gutrress yana ci gaba da cewa; Wajibi ga dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD su taka rawa fiye da wacce suke takawa a yanzu daga shekarar 2020 zuwa 2021.
Majalisar Dinkin Duniyar dai tana da dakaru a cikin kasar ta Afirka ta Tsakiya da ake kira da Minuska.
Sai dai a cikin watan Nuwamba mai zuwa ne wa'adin ayyukan dakarun zai zo karshe, don haka magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar yake son a tsawaita wa'adin aikin nasu.
Tun a 2013 ne dai Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta fada cikin matsalar tsaro wacce take ci gaba har yanzu