Oct 28, 2018 09:17 UTC
  • Masar: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 13

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ce ta sanar da cewa an kashe 'yan ta'addar ne a tsakiyar kasar

Majiyar ta ci gaba da cewa; "Yan ta'addar sun boye ne a wani wuri dake tsakanin Asyut da Kharija kudu da birnin alkahira. Sai dai sojojin kasar sun yi fito na fito da su, wanda daga karshe ya kai ga kashe 13 da cikinsu.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta ci gaba da cewa; "Yan ta'addar suna amfani da maboyar tasu ne a matsayin cibiyar ba da horo ga sabbin shiga a harkar ta'addanci. Da akwai bindigogi da abubuwa masu fashewa da aka samu a tare da 'yan ta'addar.

A ranar Larabar da ta gabata ma dai jami'an tsaron kasar sun sanar da kashe wasu 'yan ta'addar su 11 a gundumar Asyut.

A cikin shekaru biyar na bayan nan sojojin Masar suna yaki da 'yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar.

Da akwai kungiyoyin masu dauke da makamai da suke da alaka da al'ka'ida da kuma Isis ko Da'esh.

Tags