Ana Alhinin Rasuwar Mace 'Yar Jarida Ta Farko A Nijar
Kafofin yada labarai da manyan jami'ai da sauren al'umma a Nijar, na ci gaba da nuna alhini dangane da rasuwar Mariama Keita, mace ta farko data fara aikin jarida a kasar.
Shugaban kasar Mahamadu Isufu ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalen marigayiyar.
A jiya Litini ne Allah ya yi wa 'yar jarida rasuwa, kamar yadda 'yan uwanta suka sanar a kafofin yada labarai na kasar.
Maraima Keita ta rasu tana da shekara 72 a duniya bayan fama do doguwar jinya.
A wata sanarwa daga ma'aikatar sadarwa da aka fitar a gidan talabijin din kasar, an ce 'yar jaridar ta rasu ne a kasarTurkiyya.
Mirigayiyar wacce aka haifa a birnin Yamai a shekara 1946, ta taba rike mukamin shugabar gidan radio na kasa, mallakin gwamnati, (Voix du Sahel), ta kuma rike mukamin shugabar hukumar sadarwa ta kasar CSC (2003-2006).
Ko baya ga hakan ta kasance fitaciyar 'yar kungiyar fara hula data sha fafatuka wajen jagorantar kungiyoyin mata a kasar ta Nijar.