Nov 02, 2018 06:28 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Samun Bullar Tashe-Tashen Hankula A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Kungiyar Likitoci da Babu kan Iyaka ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Tashe-tashen hankula suna ci gaba da tarwatsa al'ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

A bayanin da kungiyar likitoci da babu kan iyaka ta Doctors Without Borders ta fitar a jiya Alhamis ta bayyana cewa: A wani sabon rikicin kabilanci da na addini da ya kunno kai a garin Batangafo da ke arewacin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya an samu hasarar rayukan mutane tare da jikkatan wasu adadi mai yawa baya ga tserewar mutane fiye da 10,000 daga muhallinsu.

Bayanin ya kara da cewa: Rikicin ya yi sanadiyyar tarwatsa sansanonin 'yan gudun hijira guda uku da kona gidajen jama'a gami da kasuwar garin na Batangafo.

Kungiyar likitocin ta Doctors Without Borders ta kuma fayyace cewa: Bullar wannan sabon rikici a garin na Batangafo zai kara wurga rayuwar dubban jama'a cikin halin kaka-ni ka yi musamman bullar matsalar karancin abinci da tsabtaceccen ruwan sha gami da matsuguni mai aminci.

Tags