Nov 03, 2018 06:28 UTC
  • Tattalin Arzikin Nijar Zai Habaka A Shekara 2019

Wani rahoto da asusun bayar da lamani ta duniya (IMF) ta fitar ya nuna cewa tattalin arzikin kasar Nijar zai karu da kashi 1,3% a shekara 2019 mai zuwa.

Wannan na kunshe ne a rahoton hasashen tattalin arzikin da asusun, an ce tattalin arzikin kasar zai habada daga kashi 5,2% a wannan shekara ta 2018 zuwa 6,5% a shekara 2019 mai zuwa.

Asusun ya kuma yabawa mahukuntan kasar ta Nijar, akan rawar da take kan takawa don cimma maradun habaka tattalin arzikin kasar ta hanyar shirye shirye masu yawa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin fara hula a kasar ta Nijar suka fara korafi dangane da daftarin sabuwar dokar haraji ta 2019 da gwamnatin kasar ta mikawa majalisar dokokin kasar domin neman amincewa.

Tags