Nov 03, 2018 19:13 UTC
  • Bazum: Sojojin Nijar Na Kaddamar da Farmaki Kan Sansanonin 'Yan Ta'adda

Ministan harkokin cikin gida na jamhuriyar Nijar Bazum Muhammad ya bayyana cewa, sojojin kasar suna kaddamar da farmaki a kan sansanonin 'yan ta'adda a yankunan da ke kan iyakoki a kudu maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau a gaban majalisar dokokin jamhuriyar  Nijar a birnin Yamai, ministan harkokin cikin gida na kasar Bazum Muhammad ya bayyana cewa, an tura jami'an tsaron kasar masu yawa a yankin Torodi da ke kusa da iyaka da Burkina Faso, kuma sun samu nasarar rusa sansanonin 'yan ta'adda a wurin.

Ya ci gaba da cewa, wannan farmaki da sojojin Nijar suka fara zai ci gaba, domin tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasar, ta yadda hakan zai kawo karshen kutsen da 'yan ta'adda suke yi a cikin kasar.

Kwanakin baya ne wasu 'yan ta'adda da suka shigo cikin kasar ta Nijar daga kasar Mali, suka rika karbar kudade daga mutanen kauyukan da ke wanann yanki a matsayin suna karbar zakka.

Tags