Nov 05, 2018 11:14 UTC
  • Nijar : Za'a Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Mai Aiki Da Hasken Rana A Yamai

A wani mataki na shayo kan matsalar wutar lantarki a Yamai, babban birnin kasar, gwamnatin Nijar, ta cimma wata yarjejeniya da abokan huldarta domin gina wata tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana.

Tashar da ake sa ran kammala aikinta a shekara 2021, zata samar da wutar lantarki  mai karfin Migawatt 20.

Kungiyar tarayya Turai da kungiyar samar da ci gaba ta Faransa (AFD) zasu zuba kudaden gina wannan tashar da ya kai Biliyan 18,7 na kudin CFA, kwatamcin Miliyan 28 na kudin Yuro. 

Babban darektan kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Alassane Halid, ya yaba da matakin wanda ya ce zai taimaka wa birnin na Yamai, da yake fuskantar matsalar wutar lantarkin da yake samu daga Najeriya.

Tags