Nov 11, 2018 05:37 UTC
  • Somaliya : Mutane 41 Suka Mutu A Harin Mogadisho

A Somaliya, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kai wa a Mogadisho babban birnin kasar ya 41, a cewar 'yan sanda kasar.

Tunda farko dai an bayyana cewa mutum akalla 20 ne suka rasa rayukansu a harin na ranar Juma'ar data gabata.

Saidai shugaban 'yan sandan yankin Ibrahim Mohamed, ya ce adadin mutanen da suka rasun ya haura zuwa 41, a yayin da wadanda suka jikkata sun kai 106.  

Mafi yawan wadanda lamarin ya rusa dasu fararen hula ne dake cikin wata motar bus dake kan wucewa a daidai lokacin tashin bama-baman.

Majiyoyin tsaro da ganau dai sun shaida cewa, an kai harin bam din ne da motoci guda biyu da yammacin ranar Juma'a a kusa da wani Otel mai suna Sahafi wanda ya shahara wajen karbar mayan jami'an siyasar kasar ta Somaliya.

 

Tags