Nov 11, 2018 05:38 UTC
  • Boko Haram : Shekau Ya Bayyana A Wani Sabon Bidiyo

Kungiyar Boko haram, ta fitar da wani sabon faifan bidiyo wanda ke nuna shugaban ta Abubakar Shekau, na daukan alhakin kai wasu jerin hare hare a baya bayan a arewa maso gabashin Najeriya.

Hoton bidiyon na nuna Abubakar Shekau na cewa, su ne keda alhakin kai harin baya bayan nan a kauyen Kumshe dake kusa da iyala da kasar Kamaru.

Haka zalika Shekau ya bayyana a cikin gajeren bidiyon cewa su ne keda alhakin kai hare haren wasu kauyuka da suka hada da Gulumba a baya bayan nan.

Wani abu da ya dau hankali a bidiyon shi ne yadda kungiyar tayi amfani da tambari da kuma tutar kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) reshen yammacin Afrika (ISWAP). 

Wannan dai shi ne karon farko farko da Shekau ya bayyana a wani faifan bidiyo tun bayan wanda kungiyar ta fitar a watan Yuli da ya gabata.

Tags