Nov 11, 2018 17:16 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Wasu Kwamandojin Boko Haram Su Biyu - Jami'ai

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram su biyu bugu da kari kan kwato wasu yankuna a ci gaba da kokarin fatattakan 'yan kungiyar daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ba da labarin cewa rundunar sojin ta Nijeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da wallafa a shafinta na Twitter a yau din nan Lahadi inda ta ce: sojojin sun hallaka Abu Rajal da Tuja Sa'inna Banki biyu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ta Boko Haram a lokacin da sojojin suke kakkabe yankunan Gumsuri da Gambori daga 'yan Boko Haram.

Har ila  yau sanarwar ta ce dakarun sojin sun kwace wasu kauyuka daga hannun 'yan ta'addan na Boko Haram a yayin wadannan hare-hare.

Wannan sanarwar dai tana zuwa a daidai lokacin da a kwanakin nan 'yan Boko Haram din suka  kai wasu munanan hare-hare a wasu kauyuka da suke wajen birnin Maiduguri babban birnin jihar ta Borno lamarin da ya tilasta wa mutanen garuruwan gudu don tseratar da rayukansu.

A wata sabuwa kuma runudnar sojin ta Najeriya ta sanar da sauya kwamanda mai kula da runduna mai fada da Boko Haram Janar Aba Seiko da janar Benson Akaneiro a kokarin da ake yi na ganin an kawo karshen kungiyar. Wannan sauyin dai shi ne irin sa na biyar da aka yi wa kwamandojin rundunar.

 

Tags