Nov 17, 2018 18:58 UTC
  • An Kashe Mutane 40 A Wani Harin Da Aka Kai Kan Sansanin Yan Gudun Hijira A Afrika Ta Tsakiya

Mutane kimani 40 ne suka rasa rayukansu a lokacinda aka kai hari kan sansanin yan gudun hijira a kasar Afrika ta tsakiya a ranar Alhamis da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa an kai harin ne a garin Alindao mai tazarar kilomita 300 daga Bangi babban birnin Kasar. Labarin ya kara da cewa maharin sun kona sansanin yan gudun hijiran wanda Cocin Catholica take kula da shi, wanda kuma yake dauke da yan gudun hijira kimani 20,000. 

Wani dan majalisar dokokin kasar mai wakilan yankin Alindao, Etienne Godenaha ya bayyana cewa ya ga gawaki 42 ya zuwa lokacin bada wannan labarin sannan har yanzun ana neman wadanda suka bace. Banda haka ya ce wasu yan gudun hijiran sun gudu sun shiga daji a yayinda wasu kuma suka koma wasu sansanonin yan gudun hijira da ke cikin garin. 

Najat Rochdi jami'i hukumar bada agaji ta MDD a kasar Afrika ta tsakiya 1/5 na mutanen kasar Afrika ta tsakiya miliyon 4.5 sun bar gidajensu tun farkon tashin hankalin. Sannan duk tare da cewa an gudanar da zabubbuka a shekara ta 2016 amma kasar ta ci gaba da fuskantar matsalolin siyasa da tsaro.

 

Tags