Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an Tsaron Kasar Niger Biyu A Kusa Da Kan Iyaka Da Kasar Burkina Faso
Mahukuntan Niger sun sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri a yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso, inda suka kashe jami'an tsaron kasar biyu.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Mahukunta a Jamhuriyar Niger sun sanar da kashe jami'an tsaron kasar na Jandamari guda biyu tare da jikkata wani guda a harin da gungun 'yan ta'adda suka kaddamar a yankin Makalondi da ke kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso.
Tun a karshen watan Oktoban wannan shekara ce mahukuntan Jamhuriyar Niger suka dauki matakin jibge jami'an tsaron kasar a yankunan da suke kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso da nufin dakile hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasar sakamakon ganin yadda 'yan ta'addan suke ci gaba da kai komo a kan iyakokin kasashen yankin.