Nov 18, 2018 10:09 UTC
  • Jirgin Faransa Marar Matuki Ya Fado A Nijar

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa wani jirgin sojin Faransa marar matuki ya fado a wajajen kauyen Bugum dake a yankin Torodi, kusa da birnin Yamai.

Jirgin kirar Reaper na tawagar sojin Faransa ta Barkhane, ya rikito ne bayan ya dayo daga shawagi.

Babu wata hasara da faduwar jirgin ta haifar.

Kayo yanzu kuma babu karin bayyani game da musababin faduwar jirgin.

Ma'aikatar tsaron Faransa ta tabbatar da faruwar lamarin, tare kaddamar da bincike.

Tags