Nov 24, 2018 05:51 UTC
  • Buhari Ya Tura Ministan Tsaro Zuwa Chad Don Tattauna Batun Hare-Haren Boko Haram

Shugaban Muhammadu Buhari na Nijeriya ya tura ministan tsaron kasar Birgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya zuwa kasar Chadi don gudanar da tattaunawa ta gaggawa da shugaba Idris Deby da kuma takwararsa na kasar Chadin kan sake tabarbarewar lamurran tsaro a kan iyakokin kasashen biyu da yayi sanadiyyar karuwar hare-haren da Boko Haram take kai wa yankin.

Kafar watsa labaran Eagles Online ta Nijeriya ta ce wata majiyar fadar shugaban kasar ce ta shaida mata wannan labarin, kamar yadda kuma ta ce kakakin shugaba Buharin, Garba Shehu ya tabbatar mata da shirin da ake da shi na tura ministan tsaron zuwa Chadi sai dai ya ce bai san mene ne dalilin ziyarar tasa ba.

Rahotanni dai suna nuni da cewa tura ministan tsaron na Nijeriya zuwa kasar Chadin tana da nasaba da harin ta'addancin da 'yan Boko Haram din suka kai jihar Borno inda wasu rahotannin suka kimanin sojojin Nijeriya 140 ne suka rasa rayukansu.

Kafar watsa labaran ta kara da cewa wata majiyar diplomasiyyar Nijeriya din ta shaida mata cewa Nijeriya tana da matsala da kasar Chadi cikin rundunar hadakar da aka kafa da nufin fada da 'yan kungiyar Boko Haram din da hana su kai hare-hare kan dukkanin kasashen da suke yankin Tekun Chadi.

Kasar Chadin dai tana fuskantar matsaloli na tsaro na cikin gidan lamarin da ya sanya ta janye sojojinta daga cikin sojojin da suke ba da kariya ga kan iyakokin Tekun na Chadi wanda ake ganin hakan ya taimaka wajen ba wa 'yan Boko Haram din damar ci gaba da kutsen da suke yi ga kasashen yankin musamman Nijeriya.

 

Tags