Nov 25, 2018 11:50 UTC
  • 'Yan Ta'adda Sun Sace

Majiyar hukuma daga garin Toumour da ke yankin Diffa da ke kudu maso gabacin kasar ta tabbatar da cewa; 'Yan 'ta'adda 50 ne su ka kai hari a cikin dare inda su ka yi awon gaba da 'yan mata 15

Harin na jiya asabar yana cikin mafi muni da 'yan ta'addar su ka kai a cikin jamhuriyar Nijar a kwanakin bayan nan.

A ranar alhamis din da ta gabata ma wasu 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin na Toumour inda su ka sace ma'aikatan kamfanin Foraco na faransa su 8

Kungiyar Boko Haram tana a matsayin babbar barazana ta tsaro ga kasar Nijar tare da sauren kasashen da suke makwabtaka da ita.

Suaran kasashen da suke fuskantar matsalar 'yan ta'adda sun kunshi Burkina Faso, Mali, da Najeriya.

Tags