Nov 26, 2018 17:26 UTC
  • Sojojin Saman Nijeriya Sun Kai Hare-Haren Sansanonin Boko Haram A Matsayin Martani Ga Harin Metele

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da kai wasu munanan hare-hare kan wani sansanin 'yan ta'addan Boko Haram a matsayin mayar da martani ga harin da 'yan kungiyar suka kai wani sansanin sojin Nijeriya da ke kauyen Metele na jihar Borno inda suka kashe sama da sojoji 100.

Jaridar The Vanguard ta Nijeriya din ta jiyo wata majiyar sojin tana fadin cewa hare-haren da rundunar sojin saman suka kai sansanin 'yan Boko Haram din da suke da alaka da harin na Metele yayi sanadiyyar tarwatsa  wasu gungun motocin 'yan kungiyar bugu da kari kan hallaka wani adadi nasu.

Majiyar ta kara da cewa: Rundunar sojin saman ta Nijeriya tana bin diddigin 'yan ta'addan ne inda harin da aka kai musu ta saman yayi sanadiyyar tarwatsa wasu motoci guda bakwai ciki kuwa har da wacce take dauke da manyan bindigogi da kuma kashe dukkanin 'yan ta'addan da suke cikin motocin.

Wasu rahotannin sun ce har ila yau daya daga cikin jiragen yakin rundunar sojin sama ta Nijeriya din ya ketare kan iyaka zuwa daya daga cikin kasashen makwabta don bin sahun 'yan ta'addan wadanda aka ce da wasu daga cikin kwamandojin na su ba ma 'yan Nijeriya ba ne, inda sojojin suka sami nasarar tarwatsa motocin sojin da suka sata yayin harin na Metele.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai wasu gungun 'yan ta'addan Boko Haram din suka kai hari kan sansanin sojin da ke kauyen Metele inda suka kashe sama da sojojin 100 da kuma yin gaba da makamai da wasu motoci na yaki da suke sansanin.

 

Tags