Nov 27, 2018 17:54 UTC
  • Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Boko Haram A Yankin Tekun Chadi

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kaddamar da wasu hare-hare ta sama a wasu yankuna na Tekun Chadi da aka ce sansanoni ne na 'yan kungiyar Boko Haram a ci gaba da mayar da martani ga harin ta'addancin da 'yan kungiyar suka kai wani sansanin sojin Nijeriya da yayi sanadiyyar mutuwar sama da sojoji 100.

Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo daya daga cikin 'yan jaridar da suke ba da labari kan hare-haren 'yan ta'addan a yankin na Tekun Chadi, wato Ahmed Salkida yana cewa a yau Talata jiragen yakin rundunar sojin saman Nijeriyan sun kai wasu hare-hare kan sansanonin 'yan kungiyar Boko Haram bangaren Al-Barnawi da aka fi sani da Islamic State in West Africa Province, ISWAP lamarin da ya tarwatsa 'yan ta'addan sai dai har yanzu ba a tantance irin hasarar da aka yi musu ba, inji shi.

Harin na yau dai ya biyo bayan wasu hare-haren ne da rundunar sojin sama ta Nijeriya din ta kai sansanonin 'yan Boko Haram din a jiya Litinin inda ta ce ta tarwatsa wasu motocin 'yan ta'addan da kuma kashe wani adadi na wadanda suke cikin motan

Hare-haren na sojojin saman dai yana zuwa kimanin mako guda da wani mummunan hari da 'yan Boko Haram din suka kai sansanin sojin Nijeriyan da ke garin Metele na jihar Borno inda suka kashe sama da sojoji 100 da kuma yin gaba da makamai da motocinsu.

 

Tags