Nov 28, 2018 17:29 UTC
  • Wata 'Yar Kunar Bakin Wake Ta Raunana Mutane 29 A Kasar Kamaru

Jami'an tsaron kasar Kamaru sun tabbatar da samun raunin mutane 29 sakamakon wani harin kunar bakin wake da wata mace ta kai a yau din nan Laraba a garin Amchide da ke yanki arewa mai nisa na kasar.

Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo wani jami'in tsaron kasar Kamaru da ya  so a sakaye sunansa yana fadin cewa da safiyar yau Laraba ce 'yar kunar bakin waken ta tarwatsa kanta a wata kasuwa da ke garin Amchide, wanda ke kan iyaka da Tarayyar Nijeriya, inda nan take mutane 29 suka sami raunuka, sai dai ya ce har ya zuwa yanzu dai babu wanda ya rasa ransa.

Har ila yau wasu majiyoyin sun ce sojojin da suke yankin sun bindige 'yar kunar bakin waken ta biyu kafin ta sami nasarar tayar da bama-baman da ta yi jigida da su.

Yankin dai ya sha fuskantar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram da suke shigowa daga Nijeriya zuwa kasar Kamarun, lamarin da ya tilasta wa mutanen garin na Amchide gudu da kuma barin garin. 

Wasu rahotanni sun ce kafin rikicin Boko Haram din dai garin yana da mutanen da sun kai 90,000 amma a halin yanzu mutanen da suke wajen mafi yawansu ma 'yan gudun hijira ne da suka shigo garin daga Nijeriya.

 

Tags