Nov 28, 2018 17:30 UTC
  • Buhari Ya Sha Alwashin Goyon Bayan Sojojin Nijeriya Har Sai Sun Cimma Manufarsu

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar gwamnatinsa ta kuduri aniyar kara karfafa sojojin kasar a ci gaba da fada da ta'addanci da suke yi a yankin Arewa maso Gabashin kasar, yana mai cewa gwamnatin tasa za ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen goyon bayan sojojin don cimma abin da suka sa gaba a yankin.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron hafsan hafsoshin sojin kasar da aka gudanar a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar kawo karshen rikici da rashin tsaron da ake fama da shi a yankin arewa maso gabas din da ke fuskantar ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram yana mai kiran sojojin da su ci gaba da kyakkayawan aikin da suke yi.

A yau Laraba ce dai shugaba Buharin ya kai ziyara jihar ta Borno inda  bayan ganawar da yayi da manyan jami'an sojin da suke fada da kungiyar ta Boko Haram har ila yau kuma ya kai ziyara fadar Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai sannan  kuma ya ziyarci dakarun kasar da suka ji raunuka a mummunan harin da mayakan Boko Haram suka kai sansanin soji da ke garin Metale a karshen makon da ya gabata.

Ziyarar ta shugaba Buhari dai  ta zo ne kwanaki kadan bayan 'yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare da suka kai sansanin soji da ke garin Metale na Jihar Bornon inda suka kashe sojojin sama da 100.

 

Tags