Nov 29, 2018 17:47 UTC
  • Za'a Fara Yi Wa Wasu Shugabannin 'Yan Awaren Kamaru Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta'addanci Shari'a

An sanar da ranar da za a fara yi wa wasu shugabannin 'yan awaren kasar Kamaru su 10 da aka dawo da su kasar daga Nijeriya shari'a bisa zargin gudanar da ayyukan ta'addanci wadanda ana iya yanke musu hukuncin kisa idan har aka same su da laifi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Christopher Ndong lauyan mutanen da ake zargin yana fadin hakan inda ya ce an tsaida da ranar 6 ga watan Disamba mai kamawa a matsayin ranar da za a fara shari'ar mutane 10 cikinsu kuwa har da Julius Ayuk Tabe, shugaban kungiyar 'yan awaren yankin da suke magana da harshen turancin Ingila masu fafutukan raba yankin na su da asalin kasar Kamarun.

Lauyan ya kara da cewa ana cajin mutanen ne dai laifuffuka da suka hada da ta'addanci, yada akidar ta'addanci da kokarin balle wani yanki na kasar Kamarun bugu da kari kan kokarin haifar da yakin basasa da kuma juyin juya hali kamar yadda wata kotun soji ta birnin Yaounde ta yi karin bayani.

Julius Ayuk Tabe da sauran mutanen da ake zargin suna daga cikin mutane 47 na yanki masu maganar da harshen turancin Ingilan na kasar Kamaru da aka kama su a Nijeriya da kuma mika su ga mahukuntan kasar Kamaru a watan Janairun wannan shekarar.

Daruruwan mutane ne dai ciki kuwa har da fararen hula, 'yan awaren da kuma jami'an tsaron kasar Kamarun aka kashe yayin rikicin da ya barke a kasar a kokarin da 'yan awaren suke yi na ware yankin na su daga asalin kasar Kamaru saboda zargin nuna musu wariya da ake yi.

 

Tags