Nov 30, 2018 03:36 UTC
  • Boko Haram : Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Bukaci Taimakon Duniya

Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, sun bukaci taimakon kasashen duniya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.

Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwa ta bai daya da shuwagabannin kasashen suka fitar a karshen taron da suka gudanar a birnin N'Djamena na kasar Chadi.

Sanarwar ta ce shuwagabannin da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya, da Mahammadu Issufu na Nijar da Idriss Deby na Chadi da kuma fira ministan Kamaru Philémon Yang, na bukatar taimakon duniya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram da kuma samar da tsaro a yankin tafkin Chadi.

A wata ganawa da sukayi shuwagannin sun nuna matukar damuwa akan yawaitar hare haren kungiyar a baya bayan nan, inda kuma suka sha alwashin canza salo na yaki da kungiyar ta Boko haram.

Haka kuma sun yi alkawarin yin irin wannan ganawar, wacce suke tattaunawa da manyan hafsoshin sojin rundinar hadin gwiwa ta kasashen (Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya) dake samun taimakon kasashen yamma da kuma mayakan sa kai.

 

Tags