Dec 02, 2018 17:48 UTC
  • Nijar : An Samu Raguwar Mace-Mace Sanadin Cutar AIDS

A Nijar, adadin mutanen dake mutuwa sanadin kamuwa da cutar AIDS/SIDA, ya ragu da kashi 15% daga shekara 2012 zuwa 2016, kamar yadda hukumomin kiwan lafiya na kasar suka sanar.

A bayanin da ya fitar a zagayowar ranar yaki da cutar da AIDS, ministan kiwan lafiya na kasar ta Nijar Dakta Illiasu Idi Mainasara, ya ce adadin mutanen dake mutuwar sanadin cutar ya ragu daga 4,000 zuwa 3,400 a shekarun baya bayan nan.

Kana kuma a cewar an samu dan sukuni akan yawan masu kamuwa da cutar, 'yan shekaru 15 zuwa 49, kwatancin ragowar 0,4 inda mutane kimanin 43, 000 ke rayuwa da kwayoyin cutar a kasar ta Nijar.

Haka zalika an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar ta AIDS daga 6,000 a shekara 2012 zuwa 1,761 a shekara 2016, a yayin da kuma mutanen dake rayuwa da kwayoyin cutar wadanda ke shan magani ya karu daga 11, 182 zuwa 17, 122 a shekara 2017.

Saidai a cewar Ministan abun damuwa shi ne a shekara 2016, an samu ragowar mutanen dake binciken gano ko suna dauke da cutar ko kuma A'a.

Tags