Dec 07, 2018 03:22 UTC
  • Al'Shebab Ta Kashe Manyan Sojojin Somaliya Biyu

Kungiyar Al'shebab ta dauki alhakin kai wani harin nakiya da ya yi sanadin mutuwar wasu sojojin Somaliya bakwai, ciki har da manyan sojoji guda biyu.

Rahotanni sun nuna cewa manyan sojojin da suka hada da Janar Omar Adan Hassan dake jagorantar bataliyar sojojin Somaliya ta 12 da kuma kwamandan yaki na rundinar Abdi Ali Jamame, sun gamu da ajalinsu ne a yayin da motar da suke ciki ta taka nakiya akan hanyarsu ta komawa Mogadisho, bayan wani ran gadi a wata bataliyar soji dake kudancin babban birnin.

Wasu majiyoyin soji sun tabbatar da aukuwar lamarin, wanda suka ce ya yi sanadin mutuwar manyan jami'an soji biyu da kuma wasu sojoji biyar da raunata wasu biyu.

Kungiyar Al'shebab dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaïda, ta dai jima tana kai hare hare makamantan wannan ciki harda na kunan bakin wake kan cibiyoyin gwamnati dana jami'an tsaro da kuma kan fararen hula a wannan kasa ta Somaliya ciki har da a Mogadisho babban birnin kasar.

Tags