Dec 20, 2018 19:04 UTC
  • An Kama Mutane 3 A Morocco Da Zargin Kashe Turawan Yan Yawon Shakatawa A Kasar.

Yansanda a kasar Morocco sun bada sanarwan kama mutane ukku wadanda ake tuhuma da kashe wasu mata biyu yan yankin Scandanvia yan yawon shakatawa a cikin kasar.

Shafin yanar gizo na Mairur na kasar ta Morocco ya nakalto majiyar yansanda a kasar tana cewa an kama mutane ukku dangane da wannan kissan.

Amma wadanda ake tuhuma sun musanta aikata wani laifi, sun kara da cewa su dai sun zauna suna hutu a kusa da inda aka yi kisan ne.

Labarin ya kara da cewa matan da aka kashe suna Marine Yoland yar shekara 28 a duniya daga kasar Austria, sai kuma Louisa Jaspersen yar shekara 24 a duniya wacce ta fito daga kasar Denmark. 

Ya zuwa yanzu dai ba wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin wannan mummunan kisan.

Amma duk da haka ma'aikatar tsaron kasar Denmark ta bada sanarwan cewa, mai yuwa yan kungiyar ta'adda ta Daesh suna da hannu a cikin wannan kissan. 

Tags