Dec 22, 2018 15:10 UTC
  • Somaliya : Tagwayen Hare-hare Sun Kashe Mutum 7

Rahotanni daga Somaliya na nuna da cewa akalla mutum bakwai ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren bam da aka dana a mota a kusa da fadar shugaban kasar dake Mogadisho.

Ganau sun shaidawa masu aiko da rahotanni cewa harin na farko ya auku ne a kusa da wani wurin bincike na gidan kallon wasan kwakwayo dake mita 500 a kusa da fadar shugaban kasar.

Jim kadan kuma bayan hakan wani hari wanda aka bayyana da mafi karfi, shi ma ya faru, a cewar Idil Hassan, wanda ya ce ya ga gawarwakin mutane da dama ciki har da jami'an tsaro.

Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dilancin labaren AFP, wani jami'in 'yan sanda a yankin ya ce mutum bakwai ne suka mutu a harin, kana wasu gommai suka raunana a jerin hare haren.

Wani gidan talabijin din kasar ta Somaliya mai suna (Universal TV) dake da cibiya a birnin London ya ce uku daga cikin ma'aikatansa da suka hada da dan jarida guda dan asalin kasar ta Somaliya da Biritaniya sun rasa rayukansu a hare haren.

Tuni dai kungiyar nan ta Al'shabab dake dake da alaka da kungiyar Al-Qaïda ta dauki alhakin kai hare haren wanda a cikin sanarwar data fitar ta ce, ta kai hare haren ne a wani shingen bincike dake kusa da fadar shugaban kasa.

Tags