Dec 29, 2018 19:17 UTC
  • Sojin Najeriya Sun Fatataki 'Yan Boko Haram A Garin Baga

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta fatataki 'yan Boko Haram a garin Baga dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wanann dai na zuwa bayan samun rahotannin cewa mayakan na Boko haram sun kwace garin na Baga harma da kafa tuta a garin.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Ibekunle Daramola ya fitar, ta ce bayan harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar a garin na Baga, an aike da jiragen yaki da suka fatattaki mayakan.

Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin fatatakar 'yan ta'addan.

 

Tags