Dec 30, 2018 10:37 UTC
  • Sojin Nijar Sun Hallaka Mayakan Jihadi Da Dama A Iyaka Da Mali

Rundinar sojin Nijar hadin gwiwa da rundinar Faransa ta Barkhane sun hallaka gomman mayakan dake ikirari da sunan jihadi a iyakar kasar ta Nijar da Mali.

Wata sanarwa da rundinar sojin Faransa ta fitar a cikin daren jiya ta ce wani hari da aka kai a cikin daren ranar 27 ga wata nan da jiragan yaki ciki harda masu saukar angulu kirar Tiger an hallaka mayakn jihadi kimanin15.

An dai kai harin ne kan 'yan jihadin da suka hadu a yankin a iyaka da Tongo tongo.

Rundinonin sojojin sun kuma kwace ikon sansanoni da dama da mayakan kafin gudanar da samame na tsawon sa'o'i 48 a yankin, inda suka kwato babura masu yawa da kuma makaman yaki ciki harda masu sarafa kansu..

 

Tags