Jan 10, 2019 12:23 UTC
  • Mutane Fiye Da Dubu 30 Ne Suka Kauracewa Gidajensu A Arewa Maso Gabacin Najeriya

Majiyar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar dinkin duniya a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa mutane akalla dubu 30 ne suka kauracewa gidajensu a garin Baga dake gabacin Jihar Borno a arewa maso gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Edward Kallon jami'in hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya a Najeriya yana fadar haka a jiya Laraba.

Edward ya kara da cewa a cikin makon da ya wuce kadai mutane kimani dubu 30 ne suka kauracewa gidajensu a garin Baga zuwa birnin Maiduguri inda ake da sansanonin yan gudun hijira, sanadiyyar tsananin fadan da ake fafatawa tsakanin sojojin kasar da kuma mayakan kungiyar Boko Haran a yankin.

Gwamnatin Najeriya dai ta amince akwai matsalolin yan ta'adda a yankin gabacin jihar Borno amma tace sojojin kasar sun fi karfin mayakan na Boko haram a mafi yawan yankunan jihar ta Borno idan an kwatantan da yadda aka sami yankin a lokacinda ta haw kan kujerar ikon kasar.

Tags