Jan 10, 2019 19:27 UTC
  • Boko Haram Na Ci Gaba Da Tafka Laifuka Akan Fararen Hular Najeriya

Sojojin Najeriya sun sanar da cewa; 'yan kungiyar ta Boko haram suna tilastawa fararen hula ficewa daga gidajensu da garuruwansu a yankin arewa maso gabacin kasar

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto wani bayani da sojojin na Najeriya su ka fitar da a ciki suke cewa;  'Yan kungiyar ta Boko haram sun yi kutse a wani yankin da ke kusa da birnin Maiduguri babban birnin jahar Borno

Bayanin ya ci gaba da cewa; "Yan kungiyar ta ta'addanci suna yi wa mutane barazana da tilasta su su fice daga gidajensu

Tun da fari, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa; Fiye da mutane 30,000 ne suka fice daga gidajensu domin gujewa Boko Haram a garuruwan Baga da Monguno, inda su ka shiga cikin birnin Maiduguri domin samun mafaka

Shekaru 9 kenan da kungiyar ta Boko Haram ta fara tada kayar baya a Najeriya wanda kawo ya zuwa yanzu rikicin yayin sanadin kashe mutane fiye da 20,000

Bugu da kari kungiyar ta zama barazanar tsaro ga kasashen makwabta da su ka hada Nijar, Chadi, da Kamaru

Fiye da mutane miliyan biyu ne kungiyar ta mayar 'yan gudun hijira a cikin gida da kuma waje

Tags