Jan 13, 2019 19:07 UTC
  • Najeriya: Wata Babbar Mota Ta Kashe Mutune 20 A Jihar Ekiti

Majiyar Jami'an tsaro a tarayyar Najeriya ta bayyana cewa mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansi a lokacinda wata mota babban ta burma a cikin wata kasuwa a jihar Ekiti daga kudancin kasar a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Cana ya nakalti jami'an tsaron kasar sun tabbatar da labarin, sunnan sun bayyana cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu masu saya da sayarwa ne a cikin kasuwar.

Dangane da yiyuwan ko hatsarin wani aikin ta'addanci ne wannan kuma sai abinda bincike ya tabbatar. Labarin ya kara da cewa motar tana dauke da shikafe ne wanda yake dauke da hoton wani dan takarar jam'iyyar APC a jihar. 

Wata majiyar ta bayyana cewa hatsarin ya auku  ne da misalin karfe 8 na yamma a Iworoko da jihar Ikiti bayan da direban motar ya kasa tsaida motar.

Wasu wadanda suka ganewa idanunsa sun bayana cewa adadin wadanda suka mutu ya kusan 45. 

Tags