Jan 28, 2019 07:40 UTC
  • Najeriya: Sojojin Najeriya 6 Sun Jikkata Saboda Harin Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Boko Haram

Kungiyar 'Yan ta'adda ta Boko Haram sun kai hari akan sansanoni biyu na sojojin kasar dake Jahar Borno a arewa maso gabashin kasar

Harin dai ya zo ne a lokacin da batun fada da ta'addanci yake a matsayin daya daga cikin kalubale a gaban 'yan takarar shugabancin kasar

Shugaba Muhammadu Buhari wanda yake neman a sake zabarsa karo na biyu a zaben shugaban kasar a watan Fabarairu mai zuwa, ya sha alwashin kawo karshen kungiyar ta 'yan ta'adda.

Kungiyar 'yan ta'adda wacce ta dauki makami tun a 2009 ta zama babbar barazanar tsaro ga kasar ta Najeriya da kuma kasashen makwabta

Ya zuwa yanzu mutanen da kungiyar ta kashe sun haura 20,000, yayin da wasu fiye da miliyan biyu da 600,000 su ka zama 'yan gudun hijira.

Kasashen Nijar, Kamaru, da Chadi suna daga cikin masu fama da matsalar kungiyar ta Boko haram

Tags