Jan 29, 2019 18:21 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Mutum 4 A Diffa

Rahotanni daga jihar Diffa dake gabashin Jamhuriyar Nijar na cewa, mayakan boko haram sun kashe akalla mutum hudu tare da raunata wasu da dama a wani hari da suka kai a cikin daren jiya wayewar wannan safiyar Talata a yammacin garin Bosso.

Mayakan sun kuma kone gidaje da dama da kuma wasu motoci kirar toyota guda 3 na masu dakon tattasai.

Wannan Harin dai na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan bayan ziyarar da ministan cikin gida na aksar ta Nijar, Bazoum Mohammed ya kai a jihar ta Diffa.

A kwanakin baya dai sojojin kasar ta Nijar sun yi nasara hallaka mayakan na Boko Haram kusan 300 a yankin tafkin Chadi a kusa da kogin Komadugu.

Jihar Diffa dake fama da matsalar Boko Haram, na karkashin dokar ta baci tun a watan Fabrairu na 2015.

 

Tags