Feb 01, 2019 05:53 UTC
  • Nijar :  Shugaba Isufu Ya Kori Ministan Kudinsa

Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriyar Nijar, bisa bukatar firaministan kasar, ya yi gyaran fuska a majalisar ministocin kasar, inda ya nada Mahamadu Diop a matsayin sabon ministan kudi na kasar.

Mahamadu Diop, wanda tsohon mataimakin babban bankin kasashen Afrika ta yamma, BCEAO ya maye gurbin Hasumi Masaudu, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya sanar a cikin daren jiya.

Babu dai karin bayyani kan dalilin korar ministan.

Hasumi Masaudu, wanda shi ne sakatare janar na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Nijar, ya taba rike mukamin darektan fadar shugaban kasar da kuma na yakin neman zabensa.

An dai jima ana ta yayata labarin cewa tsohon ministan kudin na da sha'awar tsayawa takara a zaben shugaban kasar karkashin jam'iyyar ta PNDS, inda tuni wasu ke ganin cewa fidda shi daga wannan mukami ya fara nuna alamu a yayin da ya rage shekaru biyu a je zaben shugaban kasar.

 

Tags