Feb 05, 2019 15:06 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Mutum 6 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu a wasu sabbin hare hare da mayakan kungiyar boko haram suka kai a kauyukan Shuwa da Kirchina, dake garin Madagali, na jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar.

Majiyoyi daga yankin sun ce mayakan sun kai hari ne a kyauyen Shuwa da misalin karfe 6 : 45 na yamma, inda sukayi ta harbe harbe da kuma jefa gurneti, lamarin da ya sa 'yan sanda dake lardin suka tsare.

Bayanai sun kuma ce mayakan sun kuma abkawa shaguna inda suka kwashi ganima, suka kuma sake motoci suka kuma kone gidaje.

Wasu bayanai na daban sun ce sojoji dake Madagali sun isa kauyen inda suka kori mayakan wadanda suka tsare cikin dajin Sambisa.

Baya ga hakan kuma mayakan sun kashe makiyaya uku a kauyen Tubba dake wajejen Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Rikicin boko haram wanda ya fara a shekara 2009, a arewa maso gabashin Najeriya, ya dai yi sanadin mutuwar mutane sama da 27,000 tare da tilastawa wasu miliyan 1,8 tsarewa daga muhallensu.

Tags