Feb 05, 2019 18:13 UTC
  • Taron Koli Na Kungiyar G5-Sahel

Shuwagabannin kasashen kungiyar G5-Sahel, sun gudanar da taronsu karo na biyar, yau a binin Ouagadugu na kasar Burkina Faso.

Taron shuwagabannin kasashen da suka hada da (Mali, Nijar, Burkina faso, Mauritaniya da kuma Chadi), ya maida hankali kan matsalar tsaro dake adabar yankin da kuma batun ci gaba na kasashen.

A yayin taron kasashen sun tattauna kan yadda za'a bullo da dabaru na mangance matsalar ta'addanci mai nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kuma kungiyar boko haram dake addabar yankin.

A baya bayan nan dai kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina Faso na fuskantar hare hare mayakan dake ikirari da sunan jihadin.

Taron na wannan karo a yayinsa shugaba Isufu Mahamadu na jamhuriya Nijar, ya mika ragamar shugabancin karba-karba na tsawan shekara guda na kungiyar ta G5-Sahel ga takwaransa na Burkina faso, Roch Marc Christian Kaboré.

Batun yadda rundinar kungiyar ta G5 Sahel zata gudanar da aikinta gadan-gadan na daga cikin batutuwan dake zaman karfen kafa ga kasashen mambobinta, duba da kudaden da ake bukata.

Tags