Feb 07, 2019 07:04 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda 146 A Kasar Burkina Faso

Kakakin dakarun tsaron kasar Burkina Faso ya sanar da hallaka 'yan ta'adda kimanin 150 a kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Lamoussa Fofana kakakin rundunar tsaron kasar Burkina Faso a jiya laraba na cewa gamayyar jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 146 a wasu sumame da sukai yankunan dake arewacin kasar.

Wannan kuma na zuwa ne a matsayin mayar da martani na kisan gillan da 'yan ta'addar suka yiwa fararen hula ranar Litinin din da ta gabata a kusa da iyakar kasar da Mali.

Kakakin rundunar tsaron kasar Burkina Faso ya kara da cewa wannan farmaki da dakarun hadin gwiwar kasar suka kaiwa 'yan ta'addar ta kasa da sama ya janyo hasara mai yawa ga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Tun a shekarar 2015 ne kasar Burkina Faso ta fara fuskantar hare-haren ta'addanci a cikin kasar musaman ma a yankunan kai iyakokin kasar da kasashen Mali da Nijer da Benin.

A cikin 'yan shekarun nan 'yan ta'adda sun tsananta kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a kasar ta Burkina Faso.

Tags