Feb 08, 2019 04:07 UTC
  • An Sake Kai Harin Ta'addanci A Burkina Faso

Rundinar Sojin kasar Burkina faso ta sanar da mutuwar mutum biyu a wani harin ta'ddanci da aka kai kan wata barikin jami'an tsaron jandarma dake yankin Kongussi a arewacin kasar.

Da yake sanar da hakan kakakin rundinar sojin kasar, Kanal Lamoussa Fofana, ya ce maharan sun kai harin ne da nufin kubutar da wani mutuminsu da ake tsare da a barikin, inda cikin harbe harbe da suke yi suka kashe fararen hula guda biyu dake tafiya a kusa da wurin.

Ya kara da cewa mutumin da maharan sukayi yunkurin kubutar wa, na daga cikin wadanda suka kai hari a bataliyar Burzanga a ranar 6 ga watan Nuwamban 2017.

Wannan harin dai shi ne irinsa na uku a cikin makon nan a kasar ta Kamaru, kuma yana zuwa ne kwanaki biyu bayan taron koli na kungiyar G5-Sahel a Ouagadugu babban birnin kasar ta Burkina faso, inda shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar suka nemi tallafin MDD, domin ci gaba da yaki da gungun mayakan dake ikirari da sunan jihadi a yankin.

Ko a ranar Talata data gabata, ranar taron na kungiyar ta G5-Sahel wani hari makamancin wannan ya yi ajalisn sojojin kasar biyar a lardin Ursi dake arewacin kasar. 

Tun a shekara 2015 ne kasar Burkina Faso ke fuskantar hare haren mayakan jihadi, wanda suka shafi har da Ouagadugu babban birnin kasar, wanda ya tilasta hukumomin kasar kafa dokar ta baci a wasu jihohi shida na kasar daga cikin 13.

Alkalumma dai sun nuna cewa mutum sama da 300 ne suka rasa rayukansu a hare haren da kasar ta fuskanta cikin shekaru hudu.

Tags