Feb 09, 2019 18:12 UTC
  • 'Yan Tawaye Sun Rungumi Zaman Lafiya A Nijar

Wasu 'yan tawaye na kungiyar (MJRN), wanda gwamnati bata amince dasu ba sun sanar da ajiye makaman yaki a yankin Dirkou

Makaman da 'yan tawayen suka mika wa hukmomin yankin, sun hada da manya da kananan bindigogi da kuma motoci.

 

Ita dai kungiyar ta MJRN, ta sanar da daukan makamai ne a shekara 2017 inda tayi barazanar kai hare hare kan cibiyoyin man fetur na Nijar, saboda abunda ta kira rashin adalci wajen raba arzikin da Allah ya hore wa kasar.

 

Tags